Gwamnan Kaduna zai kori masu gadi da ‘yan sako marasa takardun Makaranta daga aiki

Gwamnan Kaduna zai kori masu gadi da ‘yan sako marasa takardun Makaranta daga aiki

- Gwamnan Kaduna yana sallamar kananan Ma’aikata daga aiki

- A baya dai Gwamnatin Jihar ta kori Malamai sama da 21,000

- Duk Masinjan da bai da takardun Makaranta zai bar aiki a Jihar

Kawo yanzu haka Gwamnatin Jihar Kaduna na cigaba da sallamar Ma’aikatan Jihar da dama. A baya dai Gwamna Malam Nasir El-Rufai ya sallami Malaman Makaranta rututu har 21,780 da kuma Ma’aikatan kananan Hukumomin Jihar.

Gwamnan Kaduna zai kori masu gadi da ‘yan sako marasa takardun Makaranta daga aiki
Gwamnatin Jihar Kaduna na rage yawan Ma'aikata

Yanzu kuma dai Gwamnatin Jihar ta Kaduna ta shirya korar masu gadi da ‘yan sako watau masinjoji daga aiki. Gwamnan ya bada umarni cewa ayi waje da duk Ma’aikacin da ya zarce fiye da shekaru 10 yana aiki bai da takarda akalla difloma.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya za ta koyawa mutane da dama sana'a a Kano

Gwamna El-Rufai dai yana ta kokarin kawo gyara a harkar aikin Gwamnati inda yake sassabe Ma’aikata. Kwanakin baya ma dai ya shiga Hukumomi da Makarantun Gwamnatin Jihar ban da kuma Ma’aikatan Masarautu da ya kora a baya.

Idan ba ku manta ba kwanan nan wani Dattijo da aka sallama da ke aikin Masinja a Sabon-Gari Zaria ya fadi war-was. A da dai an yi tunani ya rasu amma majiyar mu ta bayyana mana cewa doguwar suma ce kurum tsohon Ma’aikacin yayi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: