Yaro mai shekaru 16 Lateef Ambudu ya gina gidan laka mai kyau a jihar Edo
- Wani matashin yaro ya gina wani gida a jihar Edo
- Dan baiwan mai shekaru 16 ya gina gidan ne da laka
Wani matashin yaro ya ba yan Najeriya da dama sha’awa bayan ya gina wani gida. An dauki hoton yaron mai shekaru 16 wanda ya gina hadadden gidan lakan a jihar Edo bayan ya kammala ginin gidan.
Yaron mai shekaru 16 wanda aka ambata a matsayin Lateef Ambudu ya nuna fasaharsa wajen gina gidan laka. Legit.ng ta ci karo da labarin matashin yaron bayan wani bidiyo nasa ya billo a Facebook.
KU KARANTA KUMA: Daure mashayan wiwi ba shi da amfani — Obasanjo
A bidiyon an gano Ambudu tsaye a gefen hadadden gidan lakan yayinda mazauna yankinsa ke ta daukarsa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng