Ana yunkurin dauke Yusuf Buhari zuwa asibitin Turai a daren yau
- A daren yau za a wuce da Yusuf Buhari zuwa asibitin Kasar Jamus
- Yusuf Buhari yayi hadari ne a saman wani babur kwanaki a Abuja
- Yanzu haka Yaron Shugaban Kasar na kwance ne a asibitin gida
Yanzu nan mu ka samu labari daga Sahara Reporters cewa za a maida Yaron Shugaban kasa Buhari zuwa asibitin kasar waje domin duba lafiyar sa. Yusuf Buhari yayi hadari ne a kan babur kwanakin baya.
Rahotanni daga Sahara Reporters sun ce yanzu haka ana kokarin daukar Yusuf Buhari zuwa asibiti a Kasar Jamus. Rahotannin sun ce Yaron Shugaban kasar ya gamu da raunuka da-dama ne bayan hadarin don haka aka kasa daukar sa zuwa kasar waje.
KU KARANTA: Mai unguwa ya kashe bakon sa ya jefa a rijiya
Jaridar Sahara Reporters tace a daren yau ake shirin shekawa da Yaron Shugaban kasar zuwa asibitin At. Josefs da ke kasar Jamus. Za a dauki Yusuf Buhari ne tare da babban Likitan Uwargidar Shugaban kasa Dakta Kamal Mohammed.
Labari ya kai gare mu kuma cewa Mahaifiyar sa watau Hajiya Aisha Muhammadu Buhari da yayar sa Halimatu Buhari-Sheriff da kuma wasu manyan Hadiman Fadar Shugaban kasa duk su na cikin wadanda za su tafi da shi zuwa Kasar waje.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng