Rundunar Sojin Najeriya ta gano wata kungiyar 'yan bindiga a Benuwe

Rundunar Sojin Najeriya ta gano wata kungiyar 'yan bindiga a Benuwe

- Rundunar sojin da aka tura kwantar da rikicin jihar Benuwe ta gano wata kungiyar 'yan bindiga da gwamnatin jihar Benuwe ke daukan nauyi mai mambobi sama da 1000

- Rahotanni sun ce ana biyan 'ya'yan kungiyar da kiran kanta 'Civilan Joint task Force' (JTF) albashin N15,000 kowanne wata duk da cewa gwamnatin jihar ta musanta hakan

- Gwamnatin jihar ta musanta daukan nauyin wata kungiyan yan bindiga sai dai ta ce gwamnatin ta kafa kungiyar masu sa ido kan dokar hana kiwon amma ba su dauke da makamai

Dakarun Sojin Najeriya da aka aike jihar Benue domin su kwanatar da tarzomar rikicin Makiyaya Fulani da Monoma a jihar sun gano wata kungiyar 'yan bindiga da ke da mambobi sama da 1000.

'Yayan kungiyar da ke kiran kanta 'Civilian Task Force' na karban albashin naira 15,000 duk wata daga gwamnatin jihar ta Benuwe duk da cewa ta musanta hakan. Dakarun bataliya na 93 na Sojin Najeriya da ke Takum ne suka yi nasarar kama mutune 9 daga cikin kungiyar.

An gano yan bindiga 1000 a garin Benuwe
An gano yan bindiga 1000 a garin Benuwe

DUBA WANNAN: Ba za mu biya albashi ga malaman da ke yajin aiki ba - Gwamna El-Rufa'i

Babban Sakataren yadda labarai na gwamnan jihar Benuwe, Mista Terver Akase ya ce gwamnatin jihar ba ta kafa wata kungiyar yan bindiga ba. Akase ya ce lokacin da gwamnan ya karbi mulki, ya tarar da kungiyar ta Civilian Task Force amma ya rushe ta kuma kawo tsarin yafiya ga matasan da suka ajiya makaman su.

Ya kara da cewa bayan kafa dokar hana kiwo a fili, gwamnatin ta kafa rundunar kula da dabobi amma ba'a ba su makamai ba kuma aikin su shine tabbatar da cewa mutane sunyi biyaya ga dokar ta hana kiwo.

Wata majiyar daga hedkwatan soji daga Abuja ta tabbatar da kama 'yan kungiyar kuma ta ce an same mutum biyar dauke da bindiga kirar AK-45 dauke da harsashi. Wadanda aka kama kuma sun tabbatar da cewa sun su 60 a sansanin su da ke Gbeyi a jihar Benuwe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164