Majalisar Wakilai ta ki amincewa da kudirin NNPC akan biyan kudin tallafin man fetur

Majalisar Wakilai ta ki amincewa da kudirin NNPC akan biyan kudin tallafin man fetur

- Majalissar Wakilai na zargin Mai Kanti Baru da biyan kudin tallafin mai

- 'Yan Majalisar sun ce ana neman biyan kudin ne ba tare da bin ka’ida ba

- Majalissar wakillai zata dawo daga hutu a ranar Talatar mako mai zuwa

Hukumar NNPC ta shiga tsaka mai wuya yayin da ake jiran majalissar wakilai ta dawo daga hutu a ranar Talatan mako mai zuwa.

Ana sa ran majalissar dattawa zata yi kaca-kaca da shugaban hukumar NNPC, Mai Kanti Baru, akan biyan kudin tallafin man fetur da yayi ba tare da bin ka’ida ba.

An riga an sanar da Kakakin majalissar wakailai, Yakubu Dogara akan wannan al’amari.

Kwamared Akinlaja Joseph, dake wakiltar mazabar Yammacin Ondo (PDP), ya fadawa manama labaru a ranar Talata cewa za su yi maganin wadanda suka sa hannu wajen biyan tallafin man fetur ba tare da bin ka’ida ba.

Majalissar Wakilai ta ki amincewa da kudirin NNPC akan biyan kudin tallafin man fetur
Majalissar Wakilai ta ki amincewa da kudirin NNPC akan biyan kudin tallafin man fetur

“Wannan shine rashin adalcin da muke magana akai, babu yadda za ayi shugabanni su yi aikin yan majalissa.

KU KARANTA : Buhari ya taba yin alkawarin cewa ba zai yi tazarce ba idan ya samu mulki - Jafar jafar

“Kowa yana da aikin sa, saboda haka wannan abu ba dai-dai bane,” inji Kwamared Akinlaja Joseph.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng