Yadda takardar kora daga aiki ta kusa zama ajalin Masinja a jihar Kaduna

Yadda takardar kora daga aiki ta kusa zama ajalin Masinja a jihar Kaduna

- Wani masinja ya fadi sumamme bayan karbar takardar kora daga aiki a jihar Kaduna

- Masinjan yana aiki ne a wata makarantar sakandire a sabongari, Zaria

- An dauke shi aiki na wucin gadi

Malam Abubakar Shu'aibu, masinja a wata makarantar sakandire dake Sabongari, Zaria, ya yanke jiki ya fadi sumamme, bayan da aka damka masa takardar sallama daga aiki.

Malam Abubakar ya shafe tsawon shekaru 11 yana aiki a makarantar kafin sallamar sa daga aiki jiya, Takara.

Yadda takardar kora daga aiki ta kusa zama ajalin Masinja a jihar Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna; Malam Nasir El-rufa'i

Wani abokin aikin Malam Abubakar ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) cewar kamar kullum sun fito aiki da safe sai aka aiko ana neman Malam Abubakar a ofishin ma'aikatar ilimi shiyyar Zaria kuma daga zuwa suka damka masa takardar sallama daga aikin.

"Bayan ya dawo sai ya nuna mana takardar sallamar sa daga aiki. Muna cikin bashi baki ne sai kawai muka ga ya yanke jiki ya fadi kasa a sume," inji abokin aikin Malam Abubakar.

DUBA WANNAN: Hukumar raya birnin Abuja za ta rushe wasu gine-gine 750

Ya kara da cewa "nan da nan hankalinmu ya tashi, muka daga shi, muka nemi wuri muka kwantar da shi muna yi masa fifita har a hankali ya fara dawowa hayyacinsa. Bayan ya dawowar hankalinsa jikinsa sai muka yanke shawarar yin karo-karon kudin da zamu ba shi ya rage zafi."

Allah ya tarfawa garin Malam Abubakar nono domin malaman makarantar sakandiren sun roki shugaban makarantar, Sa'idu Liman Umar, da ya tausaya ya dauki korarren masinjan aiki na wucin gadi, bukatar da shugaban makarantar ya amince da ita nan take. Kazalika ya ci alwashin taimakawa Malam Abubakar da wani abu dai-dai karfinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: