Bincike: Kasashe goma mafi kankantar farashin man fetur a duniya
A yayin da farashin lita guda na man fetur yake akan naira 145, ta zamto kasa ta takwas cikin jerin kasashe goma na ilahirin duniya da suke da mafi kankantar farashin a halin yanzu. Wannan farashin na N145 ya zamto daidai da kobbai 40 na mizanin dalar Amurka wato ($0.40).
A sakamakon wani bincike da aka fitar a ranar 2 ga watan Janairu na 2018, farashin man fetur a kasuwar duniya ya na a matakin $66.9 na kowace ganga guda, inda matsaikacin farashin lita guda ta man fetur ya dangana akan $1.12, wanda yayi daidai da N403.2 a kudin Najeriya.
Binciken ya kuma bayyana cewa, bambamce-bambamcen farashin man fetur a tsakanin kasashe yana faruwa ne a sakamakon kudin haraji da tallafi da gwamnatocin ke sanyawa a kasashen su.
Da sanadin wallafar jaridar The Punch a wata kididdigar bincike ta GlobalPetrolPrices.com, Legit.ng ta kawo muku jerin kasashe 10 dake sama wajen kankantar farashin man fetur a duniya.
1. Venezuela ($0.01)
2. Turkmenistan ($0.29)
3. Kuwait ($0.35)
4. Iran ($0.36)
5. Masar ($0.37)
6. Algeria ($0.37)
7. Ecuador ($0.39)
KARANTA KUMA: Osinbajo ya jagoranci taron gudanar da tattalin arziki na farko a 2018
8. Najeriya ($0.40)
9. Bahrain ($0.42)
10. Syria ($0.44)
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng