Yadda Gwamnatin Shugaba Buhari ta gyara harkar wuta a Najeriya

Yadda Gwamnatin Shugaba Buhari ta gyara harkar wuta a Najeriya

- Mun kawo irin cigaban da Buhari ya samu a wajen wutan lantarki

- Yanzu Jam’a sun tabbatar da ana samun wuta fiye da da a Kasar

- Ana sa rai wutan lantarkin ya fi samuwa a wannan shekara ta 2018

Za ku ji irin hobbasa da Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari tayi wajen gyara harkar wutar lantarki a Najeriya daga hawan ta mulki a shekara ta 2015 zuwa yanzu kamar yadda mu ka samu bayanai.

Yadda Gwamnatin Shugaba Buhari ta gyara harkar wuta a Najeriya
Ministan wuta na Gwamnatin Buhari Mista Fashola

Kawo yanzu dai abin da Najeriya ke ja na wuta ya kan haura karfin megawatts 7000. Kafin hawan wannan Gwamnati dai akwai lokacin da gaba daya abin da kasar ta ke ja ba ya haura megawatt 3000. Ana sa rai kafin 2019 a kara sama da megawatt 1000 a Kasar.

KU KARANTA: Farashin fetur a Najeriya yana cikin mafi araha a Duniya

Masoyan Shugaban kasar sun bayyana cewa haka-zalika kuma abin da kasar ke rabawa ya kai megawatts sama da 5000. Dama dai raba wutan da aka ja ya kan zama matsala a Kasar. Yanzu haka Gwamnatin Buhari tayi kokari wajen gyara wannan matsala.

Hatta dai wutan da masu jan wuta ke aikawa kamfanonin raba wuta na kasar ya karu. A 2017 sai da aka rika aika kusan megawatts 6900 a rana. A lokacin mulkin tsohon Shugaban kasa Jonathan dai mafi yawan abin da aka samu bai taba wuce megawatts 5000 ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng