Jagoran Kwankwasiyya ya samu kyakkyawar tarba a jihar Katsina (Hotuna)
A yayin wata ziyara daya kai jihar Katsina, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, kuma madugun kwankwasiyya, ya gaud a dimbin masoya, kamar yadda Legit.ng ta gano.
Masoyan sun tare Sanata Kwankwaso ne a garin Kankara, yayind a yake kan hanyarsa ta zuwa jihar Katsina, inda ya fito daga Motarsa, ya gana da masoyansa.
KU KARANTA: Sabuwar rikici ta ɓarke a jihar Taraba, sama da mutum 20 sun halaka
A ranar 30 ga watan Janairu ne ake sa ran tsohon gwamnan na jihar Kano zai kai ziyara jihar Kano don ganawa da masoyansa, karo na biyu tun bayan daya sauka daga mukamin gwamnan jihar.
Sai dai wasu masana harkar Siyasa sun danganta ziyarar da tsohon gwamnan zai kai jihar da shirin daukar damara kan burinsa na sake tsayawa takarar shugaban kasar Najeriya a shekarar 2019, inda tuni jita jita ya watsu kan cewa zai fice daga jam’iyyar APC.
Idan mai karatu zai tuna, tun bayan mika ragamar mulki ga magajinsa, Gwamna Abdullahi Ganduje, ba’a sake samun kyakkyawar dangantaka tsakanin gwamnan da Kwankwaso ba.
Ga sauran Hotunan:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng