Shugaban Kasa Buhari ya nada wani mai ba sa shawara kan tsare-tsare
- Shugaba Buhari ya nada babban mai bada shawara kan manufofi
- Dr. Mohammed A. Salisu zai rika ba Shugaban kasar shawarwari
- Dr. Adaya ya kware harkar tattali kuma yanzu zai taimakawa gida
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi wani muhimmin nadi a Gwamnatin sa kamar yadda labari ya zo mana a farkon makon nan daga Jaridar Leadership ta kasar nan. Wanda aka nada yayi fice a harkar tattalin arziki a Duniya.
Shugaba Buhari ya nada Dr. Mohammed Adaya Salisu a matsayin babban mai ba sa shawara kan maunfofi da tsare-tsaren Gwamnatin sa. Dr. Adaya mutumin Jihar Yobe ne kuma yayi karatun Digiri na farko a harkar tattali a 1982 inda ya fita da matakin farko.
KU KARANTA: PDP tayi babbar asara kwanan nan a Katsina
Dr. Adaya ya koyar a Jami’ar Lancaster a baya kuma yayi Digiri na biyu da na uku duk a harkar tattalin arziki a Jami’ar ta Lancaster da ke Kasar Ingila. Bayan nan yayi aiki da babban bankin Musulunci watau IDB da ke Birnin Jeddah a Kasar Saudi Arabia.
Kafin nan kuma yayi aiki a Bankunan Kasashen Larabawa irin su Bahrain da bankin AfDB na cigaban Afrika daga 2004 har zuwa 2014. Adaya yayi rubuce-rubuce da dama a harkar tattali inda ya kware kuma yanzu ya shirya zai taimakawa Gwamnatin Najeriya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng