Badakalar Malabu – Watanni shida kenan da Jonathan yaki amsa gayyatar da majalissar dokoki da kotu suka masa
- Tsohon shugaban kasa Jonathan yaki amsa gayyatar da majalissar dokoki ta masa watanni 6 da suka gabata
- Kwamitin majaliisar Dokoki na musamman ta na zargin gwamnatin Jonathan da karkatar da kudaden cinikin Malabu da ya kai kimanin dala biliyan daya
Watanni shida kenan bayan an gayyace shi ya zo yayi bayyani akan cinikin sayar da danyen man fetur na dala biliyan $1.1bn wanda aka fi sani da 'Malabu deal' amma har yanzu tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan, yaki amsa gayyatar da majalissar dokoki ta yi masa.
Kwamitin majaliisar Dokoki na musamman dake binciken kudaden cinikin Malabu na dala biliyan $1.1bn ta zargi gwamnatin Jonathan da karkatar kudaden.
Dan majalissar dokoki daga jihar Kwara, Mista Razak Atunwa, kuma dan jam’iyyar APC ke jagorantar bincike da kwamitin ke yi.
KU KARANTA : An kama miyagun kwayoyin da aka yi kokarin shigo da su Najeriya
Kwamitin ta gayyaci tsohon shugaban kasa, Jonathan ya gabatar da kansa gaban su a ranar 5, ga watan Yuli, shekara 2017 dan kare kansa saboda bincike ya nuna da sa hanun sa wajen karkatar da kudaden cinikin Malabu da akayi lokacin mulkin sa.
Amma tsohon shugaban kasa Jonathan bai amsa wasikar gayyatar da aka masa ba kuma ba bai tura wakili ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng