Maza masu matan aure da yawa sun fi masu mace daya tsawon rai – Tanko Yakasai

Maza masu matan aure da yawa sun fi masu mace daya tsawon rai – Tanko Yakasai

Tanko Yakasai, jigon arewa mai shekaru casa’in da daya, a garin Yakasai a jihar Kano, ya bayyana cewa maza masu mata biyu ko fiye da haka sunfi karko bisa ga masu mata daya a rayuwarsu.

Yakasai wanda ya kasance mai mata da dama da yara, ya yarda cewa kasancewa mai mata daya ya kan rage tsawon rai.

A wani hira da yayi da jaridar Punch ta tambaye shi ko yana wani aiki daban, dattijon mai shekaru 91, yace ya kasance dan aikin jarida a rayuwarsa.

Wadanda suke da yarda cewa mata daya yana rage tsammanin rayuwa basu yi daidai ba! Suna dai magana ba tare da gwaninta ba.

Maza masu mata da yawa sun fi masu mace daya tsawon rai – Tanko Yakasai
Maza masu mata da yawa sun fi masu mace daya tsawon rai – Tanko Yakasai

“Dalilai da dama suna tasiri kan tsammanin rayuwa. A wassu kasashe kamar Afghanistan, Pakistan, Iran, da sauransu, akwai matsalan talauci da jahilci.”

Yakasai wanda aka daure a gidan yari a mulkin Abacha da Babangida, ya kara da cewa, “Saboda haka, mutane basu iya bada cikakkiyar kulawa ga yaransu.

“Na karanta wata kasida a WhatsApp wanda wani gwani ya rubuta. Kasidar ta lura cewa wadanda ke aure fiye da daya sun fi masu aure daya dadewa. Na yarda da haka."

An tambayeshi kan yanda yake tafiyar da al’amarin adawa tsakanin matayensa, ya cigaba da cewa, “Wannan al’adanmu ne.

KU KARANTA KUMA: Sanata Sani ya yi watsi da Gwamna El-Rufai, ya goyi bayan malamai masu yajin aiki a Kaduna

“Ya danganta ga ko su waye. Wassu lokuta, suna kokari wajen zama da juna lafiya amman wassu lokuta suna fadace-fadace tsakaninsu. Daga nawa gwanintan,dalilin dake janyo fada itace rashin amincewar kananan wajen biyayya ga shugabancin manyan.

“Amman a wassu lokuta, su kan zauna lafiya tare da juna, hakan zaku iya dauka cewa ba miji daya suke aure ba.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng