Ya kamata ku san wadannan muhimman abubuwa guda 12 a kan tusa
- A yaren Hausa, Tusa ko Hutu, na nufin fitar da iska daga dubura
- Maza sun fi Mata yawan yin tusa
- Tusar Mata tafi ta maza wari
Duk da kasancewar kowa na yin tusa, Hausawa na ganin yin ta a gaban mutane abin kunya ne. Da yawan mutane basu san mene ne saka fitar tusa ba ko wanne amfani fitar ta ke yiwa jiki ba. Hakan ne ya saka muka kawo maku wasu muhimman abubuwa guda 12 a kan tusa kamar yadda binciken masana ya tabbatar.
1. Maza sun fi Mata yawan yin tusa
2. An fara bincike a kan tusa tun shekarar 1962
3. Mutum mai lafiya kan yi tusa a kalla sau 12 a rana
4. Adadin iskar tusa da mutum daya kan fitar a rana za ta iya cika robar balan-balan da iska
5. Fitar tusa alama ce ta kyawun aikin hanyar sarrafa abinci a ciki. Ga duk wanda baya samun yawaitar yin tusa, ya garzaya domin ganin likita.
6. Shakar iskar tusa yana da matukar mahimmanci wajen bayar da kariya ga wasu halittu dake cikin mutum saboda sinadarin Hydrogen Sulfide dake cikinta.
DUBA WANNAN: Illolin dake tattare da yi wa Mata kaciya
7. Tusar Mata tafi ta maza wari saboda yawan sinadarin Hydrogen Sulfide da tusar su ta kunsa fiye da ta Maza.
8. Tusar ku na da matukar sauri bayan fitowa daga ciki. Tana tafiyar kafa goma cikin dakika guda (10ft/sec.).
9. Tusar masu karamar kofar dubura ta fi kara saboda iskar ba ta samun wadatacciyar kofar fita.
10. Yawan taunar cingam da shan lemuka masu gas na saka mutum yawan tusa.
11. An fi yin tusa yayin bacci
12. Kiyashi ya fi kowacce dabba yawan yin tusa duk da kankantar sa. Dangin Rakuma ke biye da kiyasai wajen yin tusa, sannan sai Rakumin dawa (Zebra) da dangin Shanu.
Mutum kan ji dadi bayan fitar tusar. Yin tusa samun lafiya ne, ka saki abar ka duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng