Allah ya tona asirin wasu korarrun sojoji da suka saci mota a Kano

Allah ya tona asirin wasu korarrun sojoji da suka saci mota a Kano

Jami’an rundunar yan sandan SARS dake yakar masu fashi da makami a jihar Kano ta yi nasarar cafke barayin mota sanye da kayan sojoji.

Rundunar ta SARS ta yi nasarar cafke yan fashin ne bayan sun sace sabuwar mota kirar Hilux dada garin Fatakwal a kan hanyarsu ta tafiya jumhuriyar Nijar domin batarwa.

Allah ya tona asirin wasu korarrun sojoji da suka saci mota a Kano
Allah ya tona asirin wasu korarrun sojoji da suka saci mota a Kano

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kano DSP Magaji Musa Majia, ya bayyana cewa 'yan fashin dake sanye da kakin sojoji sun bayyana cewa su korarrun sojoji ne da aka kora lokacin da suka gujewa yaki da ta'adacci a garin Bama na Jihar Borno cikin shekarar 2016.

KU KARANTA KUMA: Za a sauya mattatun da Shugaban Kasa ya ba mukami kwanaki

Dakarun na SARS dake nan jihar Kano tare da hadin gwiwar jami'an SARS na jihar Katsina, sun samu rahotan 'yan fashin ne daga jami'an SARS na Jihar Rivers.

Allah ya tona asirin wasu korarrun sojoji da suka saci mota a Kano
Allah ya tona asirin wasu korarrun sojoji da suka saci mota a Kano

Wannan nasara da rundunar 'yan sandan Jihar Kano ta fara samu a wannan sabuwar shekara ta 2018, alamu ne na ta shiga shekarar da kafar dama wajen yaki da masu aikata miyagun laifuka musamman 'yan fashi da makami.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: