Sojojin Operation lafiya Dole sun kashe dinbin ‘Yan Boko Haram a Yankin tafkin Chadi
- An kashe ‘Yan ta’adda sama da 2,000 wajen rikicin Boko Haram
- Sojojin Kasar na cigaba da yakar ‘Yan Boko Haram a tafkin Chadi
- An kuma yi nasarar ceto dinbin Jama’a daga hannun ‘Yan ta’addan
Sojojin Najeriya sun yi wani babban kokari inda su ka kashe ‘Yan ta’adda da dama sannan kuma aka ceto Bayin Allah da ke hannun Boko Haram sama da 2000 a yakin da su ke yi a Yankin Chad.
Rundunar Sojin Najeriya na Operation Lafiya Dole ta bayyana irin kokarin da ta yi na ceto Bayin Allah da ke hannun ‘Yan ta’addan Boko Haram a tafkin Chad a hararen da su ka rika kai wa daga kwanakin baya zuwa yanzu.
KU KARANTA: An ceto wata 'Yar Chibok daga hannun 'Yan Boko Haram
Sabon Shugaban Rundunar watau Manjo Janar Rogers Nicholas ya bayyana wannan kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust. Daga cikin wadanda aka ceto dai kun ji cewa akwai wata ‘Yar Makarantar nan ta Chibok.
A cikin hare-haren da aka kai, Sojojin Kasar sun yi sanadiyyar raunata ‘Yan ta’addan na Boko Haram ban da kuma manyan makamai irin su Bindigogin AK47 da harsashai da motoci da aka karbe.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng