Kiwon Lafiya: Cututtuka goma da gwanda ke nesanta su da lafiyar dan Adam

Kiwon Lafiya: Cututtuka goma da gwanda ke nesanta su da lafiyar dan Adam

A sakamakon yalwar sunadarin Vitamin C da gwanda ta kunsa, ya sanya ta tara dumbin alfanu ga lafiyar dan Adam da ya kamata muyi riko da ita.

A yayin da wannan lokaci da muke ciki shine kakar gwanda musamman a kasar Najeriya, saboda haka babu wani cuzguni wajen nemanta domin kuwa za a same ta cikin sauki.

Ita dai gwanda ta ba iya kacin sunadarin vitamin C kadai ta kunsa ba, domin kuwa ta kunshi sunadarai dake yiwa lafiyar dan Adam garkuwa da cututtuka daban-daban. Wadannan sunadarai sun hadar da; Vitamin E, antioxidants, fibre, vitamin A, phytonutrients, papain, flavonoids, beta-carotene da makamantansu.

Gwanda
Gwanda

Legit.ng ta kawo muku jerin cututtuka goma da gwanda ke yiwa jikin dan Adam garkuwa da su a sakamakon wannan sunadarai da ta kunsa:

1. Sunadaran fibre, vitamin C da kuma antioxidants da gwanda ta kunsa su kan hana taruwa daskararren maiko a tashoshin jini. Hakan ya sanya gwanda ta zamto garkuwa da cututtukan zuciya irinsu hawan jini da bugun zuciya.

2. Rage nauyin jiki

3. Inganta garkuwar jiki ta yadda zai iya yakar cututtuka.

4. Ciwon suga

5. Inganta lafiyar gannai wato idanu

KARANTA KUMA: Illolin amfani da hodar Iblis ga lafiyar Dan Adam

6. Hana kamuwa da cutar kumburi da radadi a gabbai ta hanyar inganta lafiyar kashi

7. Ta'azzara narkewar abinci da wuri a cikin cikin dan Adam

8. Daidato tare da saukaka zubar jini da kuma radadin mara na ciwon al'ada ta mata

9. Sunadaran vitamin C, vitamin E da kuma beta-carotene da gwanda ta kunsa su kan taimaka wajen hana tamushewa da wuri a sanadiyar tsufa

10. Garkuwa da cutar daji wato kansa ta 'ya'yan hanji, maraina da kuma mahaifa

Baya ga wadannan cututtuka da gwanda ke yiwa jikin dan Adam garkuwa da su, wani bincike da aka gudanar a jami'ar Alabama ta kasar Amurka ya bayyana cewa, sundarin Vitamin C da ta kunsa ya kan taimaka wajen dauke kasalar jiki.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng