Ka cika makaryaci - Jam'iyyar APC ta fadawa Atiku Abubakar

Ka cika makaryaci - Jam'iyyar APC ta fadawa Atiku Abubakar

Mun samu labari cewa Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi kaca-kaca da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar inda ta kira sa makaryaci. Kwanaki dai Atiku ya sauya sheka zuwa Jam'iyyar adawa ta PDP.

Jam’iyyar APC ta bayyana abin da ya sa Wazirin Adamawa Atiku Abubakar ya bar ta. Atiku yayi ikirarin cewa sabawa manufofin ta, don haka ne ta sa ya bar Jam’iyyar. Wani babba a Jam’iyyar a Jihar Legas yace ba gaskiyar maganar ba kenan.

Ka cika makaryaci - Jam'iyyar APC ta fadawa Atiku Abubakar
Igbokwe yace Atiku na neman sake takara ne da Buhari a PDP

Sakataren yada labarai na Jam’iyyar a Jihar Legas Joe Igbokwe yace Atiku ya bar APC ne don yana neman mulkin Kasar ido rufe. Sai dai Atiku ya san ba zai iya doke Shugaba Buhari a zaben 2019 ba inji Mista Igbokwe don haka ya sauya sheka.

KU KARANTA: Muhimman abubuwa da su ka faru a shekarar da ta wuce

Igbokwe yace babu wasu matasa ko alkawuran APC da ke gaban Atiku kamar yadda yake kukan an yi watsi da su a Gwamnatin Buhari. Igbokwe yace Shugaban Kasa Buhari ya dauko wani aiki ne na gyara da babu abin da zai sa kuma ya koma baya.

Igbokwe yace tabbas wasu da dama za su tattara su bi tsohon Mataimakin Shugaban Kasar amma fa ba wannan ke nuna cewa zai iya lashe zabe mai zuwa ba kuma ga shekaru su na yi masa nisa kwarai da gaske don haka dole ya fara neman mafitar siyasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng