Abubuwan da Shugaban Kasa Buhari yayi wa ‘Yan Najeriya alkawari a bana
Jaridun Kasar nan na ta fashin baki game da wasu manyan alkawura da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dauka a jawabin sa na shiga sabuwar shekara. Mun kawo kadan daga cikin su:
1. Mangance matsalar fetur
Shugaban Kasar yace zai ga abin da ya turewa buzu nadi a wajen sha’anin wahalar fetur da aka yi, ya tabbatar da cewa zai yi kokarin ganin an manta da wannan matsala.
2. Hanyoyin jirgin kasa
Akwai hanyoyin jirgin kasan da yanzu aikin su ya zo karshe irin na Abuja. Bayan nan za a kammala hanyar Legas zuwa Ibadan da kuma Kano zuwa Kaduna nan da 2019. Za kuma a fara shiri gina wasu.
KU KARANTA: Abubuwa na kara sukurkucewa Jam’iyyar adawa PDP
3. Gyaran hanyoyin kasa
Kun ji cewa Gwamnatin Tarayya za ta fara gyara titunan da su ka lalace a fadin kasar nan. Za ayi wannan ne cikin watanni uku masu zuwa. Za a kuma yi wasu sababbin hanyoyi da dama a Kasar.
4. Maganar wutar lantarki
Za a kara karfin wutan kasar a shekarar nan bayan dama tuni an ga canji a wajen sha’anin lantarki. Ana shirin kammala ayyukan wuta na Mambilla, Zungeru, Kashambila da sauran su.
5. Harkar shigo da abinci
Dama wannan Gwamnati ta dage da harkar noma, yanzu haka daga shekarar nan ake so a haramta shigo da shinkafa ko ta ina cikin kasar. A baya an hana shigo da shinkafa ta kasa.
Bayan nan Shugaban Kasar yayi alkawarin kawo karshen barnar sata da garkuwa da mutane da irin su rikicin Neja-Delta duk a wannan shekarar. a jawabin sa na murnar shiga sabuwar shekara
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng