Aisha Buhari ta tarbi jariri na farko da aka haifa a wannan shekarar a Abuja
A jiya Litinin, 1 ga watan Janairu, Uwargidan shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari ta yi marhabin da haihuwar jariri na farko a shekarar 2018, a babban birnin tarayya Abuja.
Owoichoya Daniel Okpe ya kasance jariri da farko da aka haifa da misalin karfe 12:03am na ranar sabuwar shekara ga iyalan mista Okpe Joseph Onoja da misis Olufisayo Onoja.
An haifi yaron ne wanda nauyinsa ya kai fam shida a babban asibitin Bwari bayan anyi wa mahaifiyarsa tiyata.
Uwargidan Buhari wacce ta samu wakilcin mataimakiyar gwamnan jihar Flato, Misis Pauline Tallen, ta gabatar da kyauta ga yaron da iyayensa harma da kudi da ba’a fadi adadinsu ba.
KU KARANTA KUMA: Zargin kara wasu kudade a cikin kasafin kudin shekara 2018 rashin adalci ne – Gwamnatin Tarayya
Da yake magana da manema labarai a asibitin, mahaifin yaron, Mista Okpe Joseph Onoja yayi godiya ga uwargidan shugaban kasar bisa karamci da ta nuna masa da iyalinsa sannan kuma yayi addu’an Allah y aba dansu, Yusuf Buhari lafiya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng