Shugaba Buhari zai kaddamar da wasu muhimman ayyuka a ranar Alhamis
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da wasu ayyuka a ranar Alhamis
- Zai kaddamar da wajen sauke kayan jirgi na farko dake Kakuri, Kaduna
- Ana sa ran wannan aiki da za’a kaddamar da samar da akalla ayyukan yi 5000
- Har ila yau shugaban kasar zai kaddamar da sababbin jiragen kasa 10
Rahotanni sun kawo cewa a ranar Alhamis, 4 ga watan Janairu, 2018 shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da wajen sauke kayan jirgi wato Nigeria's Inland Dry Port na farko a Kakuri, jihar Kaduna.
Zai tarbi kayan jirgi daga tashar jiragen ruwa na Apapa dake jihar Lagas, ta hanyar jiragen kasa ko kuma mota.
Sannan kuma ana sanya rai zai samar da ayyukan yi akalla guda 5000.
KU KARANTA KUMA: Allah ya umurceni da na tsaya takarar shugabancin kasa - Fasto Tunde Bakare
Har ila yau shugaban kasar zai kaddamar da sababbin jiragen kasa guda 10 da kuma injinan jiragen kasa guda biyu na hukumar tashar jiragen kasa na Kaduna zuwa Abuja.
Karin hoto a kasa:
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng