Mutanen Kaduna sun shiga sabuwar shekara da mugun alhini bayan an kashe wani Sarki
Mun samu labari daga Daily Trust cewa Mutanen Kudancin Jihar Kaduna sun shiga sabuwar shekara ta 2018 ne da mugun alhini na wani babban rashi na kashe wani Sarki da aka yi a safiyar yau litinin dinnan.
‘Yan bindiga sun buga ta’asa a Yankin na Kudanacin Jihar Kaduna inda su ka kashe Mai Girma Sarki Etum na Numana Gambo Makama tare da Matar sa da ke dauke da juna biyu a lokacin a cikin tsakar daren sabuwar shekarar nan.
Wannan mummunan abu ya faru ne a gidan Sarkin da ke wani kauye a Garin Sanga a cikin Jihar Kaduna. Makasan sun shigo cikin gidan Sarkin ne kafin sallar asubar yau inda su ka kona motoci da gidan bayan sun yi barnar da su kayi.
KU KARANTA: Sama da mutane 700 su ka kubuta daga ‘Yan Boko Haram
Marigayi Mai Girma Sarki Makama dai karamin Sarki ne na Kasar kuma ya bar fadar sa ne inda ya tafi kauyen sa na Arak domin bikin sabuwar shekara. Shugaban Karamar Hukumar Bala Audu ya tabbatar da aukuwar wannan abu maras dadi.
Cikin dai wadanda aka nemi a kashe akwai ‘Dan Sarkin mai shekaru 45 a Duniya wanda yanzu haka yana gadon asibiti bai cika ba. Wadanda su ka kai harin dai sun tsere daji kamar yadda Jami’an tsaro su ka tabattar kuma ana bincike a yanzu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng