Shugaba Buhari zai gabatar da jawabi na musamman a kafafen yada labarai gobe
- Gobe ne 1 ga watan Janairun sabuwar shekarar 2018
- Shugaba Buhari zai yi jawabi na musamman a kafafen yada labarai
- An shawarci gidajen Rediyo dana talabijin da su yada jawabin
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, zai yi jawabi na musamman ga 'yan Najeriya a gobe, ranar Litinin.
Gobe ne, idan ALLAH ya kaimu, take daya ga watan sabuwar shekarar 2018. Shugaban kasa kan gabatar da jawabi na musamman a irin wannan rana.
Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayar da sanarwar cewar jawabin shugaba Buhari zai zo da misalin karfe 7:00 na safiyar gobe.
DUBA WANNAN: Jirgin kasa dauke da fasinjojin zuwa Kano ya lalace a tsakiyar daji
Kakakin na shugaban kasa ya bukaci gidajen Rediyo dana talabijin da su kasance tare da gidan talabijin na kasa (NTA) domin kawo shirin kai tsaye ga 'yan Najeriya.
Tuni dai gwamnonin jihohin Najeriya suka fara gabatar da jawabin sabuwar shekara a jihohinsu.
Ana saka ran shugaba Buhari zai yi jawabi a kan abubuwan da gwamnatinsa ke son cimma a cikin sabuwa shekarar. Tuni dai Babban kakakin shugaban kasa, Mista Femi Adesina, ya zayyana wasu nasarori 17 da gwamnatin shugaba Buhari ta samu a cikin shekarar 2017.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng