Rikicin da su ka ratsa Majalisa a wannan shekarar
- Mun kawo manyan abubuwan da su ka auku a Majalisa bana
- Daga ciki akwai rikicin Bukola Saraki da Hukumar kwastam
- Bayan nan kuma an tsige Sanata Ali Ndume daga kujerar sa
- An kuma yi ta fama wajen amincewa da kasafin kudin bana
Yayin da shekarar 2017 ta kare mun kawo wasu manyan abubuwan da su ka faru a Majalisar Dattawan Najeriya a shekarar. A bana Majalisar tayi kaurin suna wajen abubuwa da dama daga ciki har da amincewa da wasu kudirorin da su ka dade a gaban ta.
Kadan daga cikin wadannan abubuwa kamar yadda Jaridar Daily Trust ta kawo sun hada da:
1. Tsige Ndume da kuma nada Lawan
A farkon shekarar nan ne aka tsige Sanatan kudancin Borno Ali Ndume daga matsayin sa na Shugaban masu rinjaye a Majalisar aka maye gurbin sa da Sanata Ahmad Lawan na Arewacin Jihar Yobe.
KU KARANTA: An sauyawa wasu manyan Sakatarorin Tarayya ma'aikatu
2. Tantance Shugaban EFCC Ibrahim
Majalisar Dattawan Kasar ta ki amicewa da Ibrahim Magu a matsayin Shugaban Hukumar EFCC karo na biyu a wannan shekarar wanda hakan yake kan jawo magana har gobe.
3. Rikicin Shugaban Majalisa da Kwastam
An samu takaddama da Jami’an Hukumar Kwastam wajen shigo da wasu motoci da aka yi tunani na Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ne saboda rashin bin dokokin kasa.
4. Takaddamar Dino Melaye da Sahara Reporters
Jaridar Sahara Reporters tayi ikirarin cewa Sanatan Yammacin Kogi Dino Melaye bai kammala Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ba wanda hakan ya sa sai da Jami’ar ta fito ta kare tsohon Dalibin na ta.
5. Zargin ‘Yan Sanda daga Sanata Misau
Sanata Isa Hamma Misau wanda yake Wakiltar Jihar Bauchi ya zargi Sufeta Janar na ‘Yan Sanda Ibrahim K. Idris da laifuffuka da dama wanda ya sa har maganar ta kai Kotu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng