‘Yan ta’adda za su gwammace ba a haife su ba a 2018 – Buratai
- Shugaban Sojojin Najeriya yace ‘Yan ta’adda ba su da mazauna a 2018
- Janar Buratai yace ‘Yan ta’adda za su yabawa aya zaki a shekarar badi
- Babban Sojan kasar ya ja hankalin Rundunar sa su kara kintsi da kyau
Shugaban Rundunar Sojin kasar nan Janar Tukur Yusuf Buratai ya gargadi ‘Yan ta’adda a Najeriya yayin da ake shirin shiga sabuwar shekara. Buratai yace ‘Yan ta’adda za su gwammace kida da karatu a badi.
Tukur Yusuf Buratai ya bayyana wannan ne a lokacin da Rundunar Sojojin kasar tayi wani tattaki zuwa saman dutsen nan na ‘Aso Rock’. Buratai yace ‘Yan Boko Haram da sauran masu tada zaune tsaye za su yabawa aya zaki a 2018.
KU KARANTA: Janar Buratai yayi abin da babu Hafsun Sojin da ya taba yi a Najeriya
Shugaban Hafsun Sojin Kasar Lafata Janar Tukur Buratai yace Sojojin sa sun shirya fatattakar duk masu tada zaune tsaye daga Kasar nan a shekara mai zuwa. Babban Sojan ya ja hankalin Sojojin Najeriya da su shirya kare kasar a badi.
Lafata Janar Tukur Buratai yace za su kara dagewa wajen karasa ‘Yan Boko Haram da kuma masu tada kayar baya a Yankin Neja-Delta. A karshen yayi alkawarin gyara walwalan Sojojin Kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng