Hukuncin shekaru dubu goma ga wani bazambaci da ya washe mutum 40,000
- Wannan sabon hukunci dai a kasar Sayam, watau Thailand aka yanke shi
- Pudit Kittithradilok mai shekaru 34 da haihuwa ya amince cewa eh lallai ya aikata laifin
- Kotu ta yanke masa shekaru 13,275 a gidan yari
Wata babbar kotu a kasar Siam wato Thailand, ta yanke wa wani saurayi hukuncin zaman gidan kaso na shekaru 13,275. Wannan sabon hukunci dai sabon abu ne da ba'a saba gani ba a tarihin duniya.
Pudit Kittithradilok mai shekaru 34 da haihuwa ya amince cewa eh lallai ya aikata laifin zamba cikin aminci, kuma kotun ta same shi da laifin.
A irin shirin nan da ake kira 419, ko MMM, ya yi tallar zuba hannayen jari a kamfanoninsa domin cin riba, sai dai, ashe duk yaudara ce, bayan da kusan mutum 40,000 suka zuba sama da dala miliyan 160.
DUBA WANNAN: ISIL ta dauki nauyin harin kasar masar
Ya dai amshe musu kudi, inda ya ci gaba da bushasharsa, sai a watan Agusta ne lamarin ya kai masu zuba hannun jari da maka shi a kotun babban birnin watau Bangkok. Kotun ta ci shi tarar dala miliyan 40, sannan ta kwace wasu daga kamfanonin nasa domin biyan jama'a hakkokinsu.
An kuma umarci Pudit da kamfanonin sa da su biya kimanin dala miliyan 17 ga mutane 2,653 da aka gano na wanda abun ya rutsa da su, da kuma kashi 7.5 cikin dari na ribar su ta shekara zuwa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng