An kashe kibdawa kirista a jiya a cocinsu a kasar Misra, ISIL ta ce ita ta kai harin

An kashe kibdawa kirista a jiya a cocinsu a kasar Misra, ISIL ta ce ita ta kai harin

- Kungiyar ISIL ta ce ita ce ta kai harin

- Kungiyar tana kokarin kafa daular Islama a tsakanin kasashen larabawa

- Kasashen larabawa sunyi mata chaa, kuma sun kakkabe ta daga yankin

Samari dauke da manyan bindigogi ne suka kai hari a wata coci a babban birnin kasar watau Cairo, inda suka hallaka akalla mutum 14 suka kuma raunata da dama.

Kungiyar ISIS mai ikirarin kafa dauular Islama ita ta kai harin a jiya juma'a. Sai dai fahimtar yadda lamarin yake yana bukatar karin bayani...

An kashe kibdawa kirista a jiya a cocinsu a kasar Misra, ISIL ta ce ita ta kai harin
An kashe kibdawa kirista a jiya a cocinsu a kasar Misra, ISIL ta ce ita ta kai harin

Manyan cocinan Kibdawa, na kasar Misra, na yawan fuskantar hare-hare daga mayakan ISIS, wadanda suke kokarin kafa daular Islama a yankin na larabawa, da ma wasu kasashen Afirka.

Su dai kabilar Kibdu, watau Copts, sune 'yan asalin kasar ta Masar wadda larabawa suka mamaye tun karni na 7, kuma a cikin su ne aka sami dukkan fir'aunoni da suka shafe shekaru 5000 suna mulki.

Sai dai tuni sun karbi addinin masihanci, watau Kirista, kafin zuwan Islama, inda har yanzu shi suke bi a kasar, kua suna da ma nasu Fafaroman, da ma ranekun addini wadanda suka saba da na sauran turawan duniya.

DUBA WANNAN: Sabbin nade-naden shugaba Buhari harda, matattu ashe a ciki

A 'yan shekarun nan, koda yake su musulman asali da suka kwace kasar, basu hana su yin nasu addinin ba, samari masu tsananin kishin Islama, masu kiran kansu ISIL suna yawan kai musu hare-hare a wuraren ibadunsu.

Wannan na zuwa ne bayan da kasar ta masar ta tunbuke Muhammad Morsi, wanda shi yaci zabe da aka yi bayan juyin-juya hali ya kori Mubarak Husni da iyalansa a 2011.

Sai sojoji suka dawo kuma suka sake ajje tsarin Sakulanci wanda ba ruwansa da addinai, wannan shi ya bakanta wa ustazai na kasar rai, inda su kuma samarin na kungiyar ISIL suka sami dama kutsawa da nasu ra'ayiyin cikin kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng