Wani kare da baya iya tafiya ya fara kawance da wata tattabara da ba ta iya tashi

Wani kare da baya iya tafiya ya fara kawance da wata tattabara da ba ta iya tashi

- An haifi Lundy da matsalar rashin iya tafiya wacce ta samo asali da ciwon kashin bayan da yake yi

- Wata tattabara mai suna Hernan ta na daya daga cikin manyan abokanan shi

- Wurin da suke kula da Lundy sun yanke hukuncin fara dora shi akan kujerar suna turawa

Wani kare dan wata biyu a duniya kacal, ya samu matsalar rashin iya tafiya. An kai shi Mia Foundation domin a cigaba da kula da shi, wurin da yake a birnin New York, bayan an gano halin da yake ciki. Matsalar rashin tafiyar na shi na da nasaba da ciwon kashin baya da yake yi.

Wani kare da baya iya tafiya ya fara kawance da wata tattabara da ba ta iya tashi

Wani kare da baya iya tafiya ya fara kawance da wata tattabara da ba ta iya tashi
Source: Facebook

Wannan lamari na shi dai ba abu bane na jin dadi, amma kuma cikin ikon Allah wannan larura tashi sai ta zame masa sanadiyyar samun kawa da wata tattabara da ita ma ba ta iya tashi sama.

Sue Rogers, wacce ta samar da Mia Foundation din, ta ce:

"Na dora Herman akan gado na fara lura da Lundy, bayan na gama kula dashi na dora shi kusa da Herman. Kawai sai gani nayi sun fara kula juna ta hanya mai ban sha'awa."

KU KARANTA: Kare ya ceto wata mage da suka jima suna abota tare daga wani gida da gobara ta kama

Abinda Roger ta sanya a gaba shine ta samawa karen lafiya, wajen dora shi akan kujera. Sannan kuma suna so su samo mishi wadanda za su dauki nauyin shi.

Roger dai ta kware matuka a fannin taimakon dabbobi da aka haifa da nakasa. Ba dan taimakonta ba da yawa daga cikin dabbobi sun mutu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel