Kisan gilla: Labarin wata mata da mijinta ya mutu a hannunta bayan Boko Haram sun harbe shi

Kisan gilla: Labarin wata mata da mijinta ya mutu a hannunta bayan Boko Haram sun harbe shi

- Sun kashe wa matar miji ne saboda yana aikin gwamnati

- Ta zama bazawara da 'ya'ya mata bakwai

- Sun shiga kuncin rayuwa saboda rashin masu taimaka masu

Wata mazauniyar jihar Borno ta bayyana yadda mayakan kungiyar suka yiwa mijinta kisan gilla saboda kawai ya kasance ma'aikacin gwamnati. Matar, da majiyar mu bata ambaci sunanta ba, ta ce a hannunta mijinta ya mutu bayan 'yan kungiyar ta Boko Haram sun harbe shi.

Kisan gilla: Labarin wata mata da mijinta ya mutu a hannunta bayan Boko Haram sun harbe shi
Kisan gilla: Labarin wata mata da mijinta ya mutu a hannunta bayan Boko Haram sun harbe shi

"Mijina yana zaune a daki suka shigo har cikin gidanmu suka harbe shi. Abokinsa da suke tare ma basu barshi ba domin sun bi shi duk da ya gudu, sun cimmasa a kan titi kuma shi ma sun harbe shi. Haka inaji ina gani mijina ya mutu a hannayena cikin jini," kamar yadda matar ta bayyana.

DUBA WANNAN: Muhimman abubuwa 6 da ya kamata ka sani game da Sheikh Abdulrahman As-Sudais

Matar ta cigaba da cewa "Mijina ya mutu ya barni da 'ya'ya Mata bakwai. Daya daga cikinsu na karatu a kwalejin koyon aikin lafiya, daya kuma ta gama makarantar sakandire. 'Yan Boko Haram basa son ganin 'yan mata a waje, saboda haka na dauki wahalar fita domin neman abinda zan rufawa 'ya'yana asiri."

Wannan baiwar Allah ta ce haka rayuwar ta da ta 'ya'yanta ta fada cikin mawuyacin hali tun bayan kashe mijinta shekaru biyar da suka wuce.

Matar ta nuna godiyar ta ga ubangiji da ya bata karfin daukar dawainiyar yaranta.

Tun kafin zamansu gagarumar kungiyar ta'addanci, kungiyar Boko Haram ta fara yaki ne da ilimin Boko tare da kira ga masu aikin gwamnati da su ajiye aikinsu, domin a cewar su karatun Boko da aikin gwamnati haramun ne.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: