Dandalin Kannywood: Jamila Nagudu ta bayyana matsayar ta game da korar Rahma Sadau
Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa dake yi wa lakani da Kannywood watau Jamila Umar wadda aka fi sani da Jamila Nagudu ta bayyana matsayar ta game da kin dake dakatarwar da akayi wa Rahma Sadau daga harkokin fina-finai duk kuwa da hakuri tare da nadamar da tayi.
Jarumar ta bayyana hakan ne a yayin da take ansa tambayoyi daga wasu matambaya a shafinta na dandalin sada zumunta na Facebook.
Legit.ng ta samu dai cewa wani bawan Allah ne yayi mata tambaya kamar haka: "Abinda yafi jan hankali a kannywood yanzu shine, rigimar da akeyi tsakanin Ali Nuhu da kungiyar Moppan akan korar kare da akayiwa Rahma Sadau, Saboda wani hoton bidiyo da suka yo da mawaki Classiq. Duk da jarumar ta bayar da hakuri kuma ta nemi afuwar Gwabna Dr Abdullahi Umar Ganduje da Mai Martaba Sunusi Lamido Sunusu II, amma anyi watsi da ita. Menene ra'ayin ki akan wannan dambarwa?
Sai jarumar ta kada baki tace: "Gaskiya ara'ayina abinda akayiwa Rahma Sadau ya yi tsauri da yawa. Domin duk wanda ya yi laifi ya gane kuskuren sa ya kamata ayi masa afuwa. Kuma suma Moppan din ai suna laifi. Wallahi da zamu tona masu asiri suma duk sai an canja shuwagaban nin kungiyar. Dan dai kawai tonon silili ba shi da kyau ne."
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng