Dandalin Kannywood: Fina-finan Kannywood 5 da suka yi fice a shekarar 2017
Duk da babban kalubalen matsalar satar fasaha da masana'antar finafinan Kannywood ke fuskanta, amma an fitar da fina-finai da dama a cikin shekarar 2017, da suka kunshi masu kayatarwa da marar kyau da matsakaita.
Legit.ng ta tattaro maku wasu daga cikin wadan da suka yi fice a shekarar dake bankwana nan da yan kwanaki.
1. Ankon Biki
Ali Gumzak ne daraktan Fim din, kuma Ankon Biki ya mayar da hankali ne a kan muhimmin batu da ake fuskanta a yanzu.
Mubarak (Adam Zango) da Fa'iza (Sadiya Bulala) suna shirin aure, sai Fa'iza ta kawo batun "Anko" da bukatar a hada wani babban bikin kasaita a wani wuri mai tsada.
Mubarak da abokansa sun yi iya kokarin ganin sun biya bukatar Amarya da kawayenta amma sun gagara, amma Amaryar ta dage a kan bukatar har ta bayar da kanta a madadin kudin kama wajen da za a yi bikin.
Ya fasa aurenta a ranar bikin bayan asirinta ya tonu, kuma a madadinta ya auri kawarta ta kud da kud. Fim din ya nuna girman nisan da wasu mata ke dauka don cimma bukatunsu.
2. Rariya
Yaseen Auwal ne Daraktan Rariya, kuma fim na farko da Rahama Sadau ta dauki nauyin fitowarsa, wato matsayin furodusa.
Labarin Fim din ya danganta tasirin wayar salula ta zamani da ake kira "komi da ruwanka". Fim din ya shafi yadda wasu 'yan matan Jami'a ke amfani da wayar salula domin janyo hankalin maza.
Yadda aka hada fim din ya kayatar. Babban muhimmin abu shi ne yadda daya daga cikin 'yan matan ta banbanta da saura inda har ta yi kokarin kammala karatunta.
Mutane da dama ba za su so haka ba, musamman iyaye da ke da'awar karatun 'ya'ya mata. Amma duk da haka linzamin labarin ya shafi abin da ke faruwa kuma ke shafar jama'a.
3. Mijin Yarinya
Ali Gumzak ne Darakta, kuma Mijin Yarinya ya shafi labarin wani Dattijo Attajiri Bashir Nayaya (Alhaji).
Wata rana ya ji matansa guda biyu da Allah bai ba su haihuwa ba suna ma shi addu'ar mutuwa domin gadon dukiyarsa kuma don su aure yara samari, su yi sabuwar rayuwa.
Saboda haka ne ya je ya auri budurwa Maryam Yahaya bayan ya saye imanin iyayenta da saurayinta da kudi.
Wannan ne ya fusata manyan 'ya'yansa Aminu Sharif da Sadiya Bulala, inda suka taya iyayensu mata kishi.
Bayan shafe lokaci ana makirci da takaddama, Alhaji ya yanke shawarar sakin dukkanin matansa, hadi da amaryarsa. Fim din na kunshe da darussa masu yawa a yadda aka tsara fim din.
4. Kalan Dangi
Wannan ma wani fim ne na barkwanci da Ali Gumzak ya bada umurni wato a matsayin Darakta, Fim din ya nuna yadda talakawa ke neman arziki da kuma attajirai.
Yayin da kuma masu arzikin ke kaskanta Talakawa. Ali Nuhu da Aminu Sharif da Sadiq Sani Sadiq da Jamila Nagudu da Fati Washa da Aisha Tsamiya na rayuwa ne ta nuna arziki da karya da makirci da nuna karfin iko. Idan kana neman nishadantarwa, to ka nemi Kalan Dangi.
5. Mansoor
Fim din Mansoor na FKD yana cikin wadanda ake kururutawa a matsayin gwarzon shekara. Ali Nuhu ne Darakta.
An fara fim din ne da soyayyar wasu matasa daliban makaranta, Maryam Yahaya da Umar M. Sharif.
Amma mahaifin Sharif ne ya kawo karshen abotar, saboda yana zargin Sharif ba ya da uba, wanda wannan ya ba shi kwarin guiwar gudanar da bincike domin gano asalin mahaifinsa, ba tare da sanin cewa ashe gwamnan jiha ba ne mahaifinsa.
Labari ne ya mamaye fim din. Kuma ko shakka babu, fim din ya kasance kamar a zahiri. Baki dayan fim din ya shafi labarin matasan masoya tsakaninsu da iyayensu.
An aiwatar da fim din da kyau. Taurarin fim din sun hada da Ali Nuhu da Abba El Mustapha da Baballe Hayatu da Teema Yola da dai sauransu.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng