Amfani 10 da Goro ke yi a jikin Dan Adam

Amfani 10 da Goro ke yi a jikin Dan Adam

Kamar yadda yake a wannan zamani da zaran an gano mutun dauke da goro yana cit oh, jama’a zasu fara yi masa kallon bakauye ko kuma wanda bai waye ba.

Mafi aksari anfi sanin tsoffin mutane da ta’ammali da goro. Haka zalika wasu mutane kan soki cin goro saboda yadda yake canja kalar hakora zuwa launin ja.

Daga baya ma wasu da yawa na ganin cin goro na da matukar illa ga lafiyar mai ci.

Ita dai goro aba ce da ake yin amfani da ita musamman a al’adun mutanen kasashen Afrika. A Najeriya, ana yi amfani da Shi wajen kulla zumuci da bukukuwa da ya shafi aure da karrama baki.

Amfani 10 da Goro ke yi a jikin Dan Adam
Amfani 10 da Goro ke yi a jikin Dan Adam

Wasu likitoci sun yi kokarin wayar da kawunan mutane game da amfani da ita macen goro ta ke da shi a jikin dan Adam.

KU KARANTA KUMA: Abinda muka tattauna da Buhari – Abdulmumini Jibrin

Likitoci da suka yi bincike kan amfanin goro sun bayyana cewa daya daga cikin amfanin da goro yake yi ya hada da gyara huhun mai shan taba sigari.

1. Magance ciwon kai musamman wanda ake kira da ‘Migrain headache’

2. Goro na maganin lalurar zawo

3. Tana tafiyar da gajiya.

4. Goro na rage kiba musamman ga wadanda suke fama da ita.

5. Tana taimaka wa mutanen da suke fama da kasala saboda tana duke sa sinadarin ‘Caffen’.

6. Tana hana yin amai.

7. Tana kawar da jiri.

8. Goro na maganin ciwon dajin ‘ya’yan marainan namiji

9. Yana maganin mura da cutukan da ya shafi makogoro da hanci

10. Yana hana kamuwa da cutuka

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng