Kiwon Lafiya: Amfanin kifi ga lafiyar kananan yara
A wani bincike da aka gudanar a jami'ar babban birnin Philadelphia na jihar Pennsylvania dake kasar Amurka, masana kiwon lafiya sun bayyana cewa, kananan yara dake cin kifi koda sau guda a cikin mako yana kara musu kaifin basira tare da dadada musu bacci.
Binciken masana kiwon lafiyar ya bayyana cewa, sunadarin omega-3 fatty acids dake kunshe cikin kifi shine musabbabin kara kaifin basira ga kananan yara sakamakon sanya nagartar bacci da yake assasawa yaran.
Wata masaniyar abinci ta jami'ar New York dake kasar Amurka, Samantha Heller ta bayyana cewa, duba da amfani dake tattare a cikin kifi, ana kuma bukatar amfani da shi daidai misali domin kuwa komai yayi yawa ya kan iya zamtowa cuta.
KARANTA KUMA: Na sadaukar da kaina wajen samar da ci gaba a yankin Kudu Maso Gabas - Buhari
Samantha take cewa, duk da cewar sunadarin omega-3 fatty acids dake cikin kifi ya kan kara kaifin basira ta hanyar sanya nagartaccen bacci, akwai kuma sunadaran mercury wanda wani nau'i ne neurotoxin dake illata lafiyar dan Adam.
Binciken da aka wallafa a mujallar Scientific Reports a ranar 21 ga watan Dasumba ya bayyana cewa, kifi ya kan karfafa gannai na dan Adam, inganta lafiyar zuciya da kuma kwakwalwa.
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng