An kama dan shekaru 50 da laifin yiwa mai tabin hankali ciki
- Hukumar yan sanda ta cafke wani dattijo dan shekara 50 da laifin yiwa wata mai tabin hankali ciki
- Wannan lamarin ya faru ne a garin Saniyar Jino da ke karamar hukumar kankara na jihar Katsina
- Mutumin mai suna Sufiyanu Kamala ya rika janyo hankali matar ne zuwa gonar sa inda yake lalata da ita
Wani tsoho mai shekaru 50 a duniya, Sufiyanu Kamala ya shiga hannun hukuma bisa laifin dirka ma wata mahaukaciya mai shekaru 25 ciki. Lamarin dai ya faru ne a garin Saniyar Jino da karamar hukumar kankara na Jihar Katsina.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, DSP Gambo Isah ya tabbatar da afkuwar lamarin a yayin da yake jawabi ga manema labarai a jihar inda ya ce a a halin yanzu cikin ya kai watanni 7.
KU KARANTA: Bincike ya nuna a kala 'yan sanda 221 ke hidima ga kowane gwamna a Najeriya
DSP Isah yace Sufiyanu Kamala ya janyo hankalin mahaukaciyar ne zuwa gonar sa inda ya rika aikata lalata da ita a lokuta daban-daban har abin ya yi sanidiyar shugar ciki.
Har ila yau, Jami'in na hulda da jama'a ya bada sanarwan kama wani mutum mai suna Ahmadu Yahaya mai shekaru 45 a duniya wanda aka samu da laifin keda hadin karamar yarinya yar shekaru 5 a duniya.
DSP Isah ya ce Ahmadu yana Ahmadu ya yi ma yarinyar dabara ne kuma ya shigar da ita shagon injin nikar sa inda yayi lalata da ita.
Isha ya ce mutanen biyu, Sufiyan Kamala da Ahmadu Yahaya duk suna tsare a wajen yan sanda kuma za'a gurfanar da su a gaban kotu domin su fuskanci shari'a
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng