Jerin wayoyin salular da za a dakatar daga zauren WhatsApp a 2018

Jerin wayoyin salular da za a dakatar daga zauren WhatsApp a 2018

- Masu wayoyin blackberry za su daina amfani da WhatsaApp

- Haka zalika masu amfani da wayoyin windows na zamanin da

- Ya zama dole masu Nokia su fara shirin neman wata salular

Ku na da labari dadadde cewa a farkon shekarar nan ne za a haramtawa wasu daga cikin wayoyin zamani amfani da manhajar WhatsApp domin sada zumunta ta yanar gizo saboda wasu dalilai.

Jerin wayoyin salular da za a dakatar daga zauren WhatsApp a 2018
Wasu wayoyi ba za su cigaba da aiki da WhatsApp ba
Asali: Facebook

Daga farkon Junairun sabuwar shekara ta 2018 za a dakatar da wasu wayoyi amfani da zauren WhatsApp har abada. Wayoyi masu kirar Windows na 8.0 da kuma duk wayoyin Blackberry ba za su cigaba da aiki da WhatsApp ba.

Tun a shekarar 2016 aka fara barazanar hana irin wadannan wayoyi amfani da zauren WhatsApp, daga baya ne dai aka kara wa’adin da aka bada na watanni 6. Dama tuni an dakatar da wasu wayoyin Nokia na Symbian da S60.

KU KARANTA: Najeriya za ta shigo da wasu makudan kaya ta ruwa

Har yanzu masu Nokia S40 na cigaba da more tsofaffin WhatsApp a wayar su amma nan gaba kadan za a daina aiki da su. Tun ba yau ba dai Kamfanin WhatsApp ta janye hannun ta daga wadannan wayoyi da aka bari a baya.

Masu wayar Blackberry 10 da sauran tsofaffin wayar da kuma dukkanin Nokia S40 da masu wayoyin Windows na zamanin da dole su nemi sababbin wayoyi irin su Apple da Android domin hawa WhatsApp daga Junairun 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng