Kannywood : Yan wasan da aka fi jin su a 2017

Kannywood : Yan wasan da aka fi jin su a 2017

- Legit.ng ta bayyana yan wasan kannywood da aka fi jin su a cikin wannan shekara

- An kawo sunayen su ne bisa irin rawan da suka taka a farfajiyar Kannywood

- A cikin akwai Zango, Ali Nuhu, Rahma Sadau da sauran su

A lokacin da muka gabato karshen shekara 2017, Legit.ng ta kawo muku jerin sunayen jaruman Kanywood da aka fi jin su a cikin wannan shekara.

Adam A Zango – Adam Zango yana daga cikin yan wasan da suka fi shanawa a fina-finan Kannywood a cikin shekara 2017, kuma Adamu yayi matukar burgewa wajen rera wakoki da rawa.

Bayan haka Adamu ya fito aka kafofin sada zumunta ya koka akan yadda wasu ke masa zagon kasa a harkar sa, kuma yayi alkwarin takawa duk wanda yake neman sa da rigima birki.

Rahama Sadau – Idan ana maganar yin sharihi ne a Kannywood tabbas sai suna Rahama ya fito, Rahama jaruma kuma tauraruwa ce dake shanawa a farfajiyar fina-finai, ba Hausa kadai ba har da na turanci. Rahama ta daya daga cikin yan wasa da aka ji su a cikin wannan shekara.

Ummah Shehu – A cikin wannan shekara ba a bar Ummah a baya ba, Ummah Shehu ta kara yin suna a farfajiyar Kannywood bayan katobarar da tayi akan tambayoyi da aka mata dangane da addini. Umma ta shiga tsaka mai wuya inda mutane suka ta sukar akan rashin iya amsa tambayoyi game da addinin musulunci.

Kannywood - Yan wasan da aka fi jin su a 2017
Kannywood - Yan wasan da aka fi jin su a 2017

Ali Nuhu – Ali Nuhu wanda aka fi sani da sarki baya bukatar doguwar bayyanai akan sa, saboda Sarki Ali Nuhu bashi da na biyu a Kannywood. A cikin wannan shekara sarki ya anshi kyautar giramawa a kasar Birtaniya.

KU KARANTA : 'Yan Kannywood sun zama dankali sha kushe - Hadiza Mohammed

Sadiq Sani Sadiq – Idan dai shiri na bukatar jarumi da ya kware, ka nemi Sadiq. A 2017 Sadiq yayi abun yabo. Daga wasu shiri da basu kai ga zuwa fitowa ba kamar su dan Iya, Gimbiya sailuba da sauran su, Sadiq ya nuna kwarewar sa matuka.

Nafisa Abdullahi – Nafisa, kyakkyawar yarinyar son kowa kin wanda ya rasa. A shekarar 2017 Nafisa ta dawo daga hutun sannan ta koma harkar fim. Idan dai ana maganar saka hoto a Instagram to Nafisa ta daga tuta wannan fannin.

Fati Washa – Fati Washa ta na daga cikin yan wasan da suka shana a wannan shekara. Akwai manyan finafinai da aka tallata su a wannan shekara inda wasunsu ma har sun fito.

Maryam Yahaya – Maryam Yahaya itace Karama amma kuma mai gallaza wa manya azaba. Idan baka gane ba kalli fim din Mijin yarinya. Duk da dai sabuwar fitowa ce a harkar finafinai ta na shanawa a farfajiyar finafinan Hausa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng