Zaben 2019: Guguwar siyasa ta fara kadawa akan kujerar gwamnan jihar Katsina

Zaben 2019: Guguwar siyasa ta fara kadawa akan kujerar gwamnan jihar Katsina

A yayin da shekarar 2019 ke kara gabatowa, kasar Najeriya ta fara dandanon alamu na shirye-shiryen zaben kasa da za a gudanar a shekarar, inda 'yan gwagwarmayar neman shugabanci a jihar Katsina ke sake daura damara tare da kulla silken yaki domin fafutika da kuma hankoron tsayawa takarar kujerar gwamna a jam'iyyunsu.

Akwai kimanin sama da shekara guda kafin wakanar zaben kasa na gaba, amma hakan bai sanya 'yan siyasa sunyi jinkiri wajen fara gudanar da kwankwashen kofofi da tuntube-tuntube dake da manufar kafa sabuwar kungiyoyi domin tabbatar an tsayar dasu a matsayin 'yan takara na manyan kujeru a fadin kasar nan.

A jihar Katsina, kujerar dake fuskantar rubdugu na hankoron wanda zai haye kanta itace kujerar gwamna, inda rahotanni suka bayyana cewa tuni mutane da dama sun fara gudanar da tuntube-tunube domin samun tikitin jam'iyyunsu na tsayawa takara a zaben 2019.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari

Maruwaita daga jaridar The Guardian sun bayyana cewa, jam'iyyun PDP (People's Democratic Party), APC (All People's Congress) da kuma PDM (People's Democratic Movement) suke kan gaba a yayin da mutane biyar ke gogayya da juna wajen bayyana sha'awarsu ta tsayawa takara a jam'iyyar PDP kadai wadanda suke hadar da:

1. Umar Abdullahi Tsauri, na karamar hukumar Dutsinma wanda yafi shahara da sunan Tata.

2. Abdullahi Garba Faskari, daga karamar hukumar Faskari kuma tsohon mataimakin gwamna ga tsohon gwamnan jihar, Alhaji Shehu Shema.

3. Injiniya Musa Nashuni, na karamar hukumar Kankia kuma tsohon kwamishina a tsohuwar gwamnatin Shema.

4. Mutakka Rabe Darma, daga karamar hukumar cikin birnin jihar Katsina kuma tsohon kwamishina a gwamnatin Marigayi Umaru Musa Yar'Adua.

5. Ahmed Aminu Yar'Adua, wanda dan uwa ne ga marigayi Umaru kuma tsohon sakataren gwamnatin Shema.

KARANTA KUMA: Kururuwa ta biyo bayan ci gaba da takkadamar shugabannin hidima na Najeriya

A jam'iyyar APC kuma, akwai 'yan takara 3 dake hankoron kujerar ta gwamna da suka hadar da:

1. Dakta Usman Bugaje, na karamar hukumar cikin birni kuma tsohon dan majalisar wakilai.

2. Abdulaziz Musa Yar'Adua (Audu Soja), wanda kani ne ga marigayi tsohon shugaban kasa Umaru.

3. Aminu Bello Masari, wanda shine ke rike da kujerar gwamna a halin yanzu kuma ya fito ne daga karamar hukumar Kafur.

Sai kuma jam'iyyar PDM inda Sanata Yakubu Lado Danmarke, ke kokarin bujuro da tasa manufar kuma haifaffan karamar hukumar Kankara.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: