Ta’addanci: Babban jami’in leken asiri na kungiyar Boko Haram ya fallasa kwai

Ta’addanci: Babban jami’in leken asiri na kungiyar Boko Haram ya fallasa kwai

- Babban jami’in leken asiri na Boko Haram ya bayyana abin da ya janyo baraka tsakanin Shekau da sauransu

- Tsohon jami'in ya ce Shekau ya sani cewa wata rana zai gurfana a gaban Allah, kuma zai yi bayanin zanuban da ya aikata a duniya

- Babu wata aya a cikin Alkur’ani mai girma inda Allah ya yarda da kisan wani dan Adam

Tsohon babban kwamandan kungiyar Boko Haram kuma shugaban leken asiri, AbdulKadir Abubakar wanda aka fi sani da Abu Muhammad ya bukaci shugaban kungiyar ‘yan ta’addan, Abubakar Shekau da ya daina yaudarar ‘yan mata suna tarwatsa kansu da sunan addini a kunar bakin wake.

Tsohon kwamandan ya kuma bukaci sauran shugabannin kungiyar irin su Mamman Nur da Abbor Mainok da Abu Musad Albarnawi da kuma Abbah Minok da su nizanci wannan mummunan akidar ta’addanci.

Abubakar ya kasance daya daga cikin jagororin kungiyar Boko Haram har zuwa lokacin da ya shiga hannun sojoji a watan Yuni da ta gabata a wani musayar wuta da suka yi a garin Buni Yadi wanda ke karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.

Ta’addanci: Babban jami’in leken asiri na Boko Haram ya fallasa kwai
Tsohon babban jami’in leken asirin kungiyar Boko Haram, AbdulKadir Abubakar

A tattaunawa da majiyar Legit.ng daga gidan yarin da aka tsare shi a Maiduguri, tsohon babban kwamandan leken asirin ya kuma nuna rashin amincewarsa a kan yadda Abubakar Shekau ke sa a kamo ‘yan mata tare da wanke musu kwakwalwa sannan a yi amfani da su wajen kunar bakin wake.

Abubakar ya ce: “Ina kiran dukkanin shugaban kungiyar Boko Haram da su mika wuya su dakatar da kashe-kashen da ba zai amfane su ba. Mugunta da rashin tausayin abubakar Shekau na dada ci gaba da bayyana, ya kashe mutane da dama da lalata dukiyoyi na miliyoyin naira, yayin da wasu jama’a da dama kuma sun rasa gidajensu.”

KU KARANTA: Buratai ya karfafa ma sojoji dake yaki da Boko Haram gwiwa (hotuna)

“Irin wadannan kashe-kashe na rashin imani da tausayi wanda bai bar yara da tsofaffi ba, ya sa yawancin kwamandojinsa suka gudu daga bangarensa.”

“Yaran gidansa na yi wa mata fyade da sauran munanan ta’asa, amma ko a jikinsa, kuma duk wanda ya bada shawara akan a yi gyara nan take zai bada umarnin kashe shi.”

“Shekau ya bada umarni a kashe wasu kwamandoji irin su Aliyu da babban makaniken kungiyar wanda aka fi sani da “Paper” saboda sun nemi alfarma a ba wasu mata da yara abinci lokacin da aka samu karancin abinci a sansanin Abiso.”

“A wannan lokacin mata sun zama mabarata domin samun abincin da za su ciyar da ‘ya’yansu, yara fiye 13 suka mutu sakamakon yunwa da cututtukan da ya shafi yunwa.”

KU KARANTA: Hukumar ‘yan sanda ta sallami jami’inta da ya kashe wani direba a Kogi

“Irin wadannan halayan ya sanya wasu daga cikin shugabanin kungiyar irin su Mamman Nur da Albarnawi da Man Chari da Abbor Minok da Abba Albarnawi da kuma ni kai na muka kaurace wa Abubakar Shekau doimin kafa namu bangaren, Mamman Nur ya tsallaka kasar Chadi yayin da Albarnawi da Abbah (dan autan Marigayi Muhammad Yusuf) suka tsaya a Magumeri."

“Mu da kanmu kamar sojojin Najeriya muna farautar Shekau domin mugayen aiyukkan da ya tafka da sunan mu, mun fafata da shi har sau tara, inda muka magoya bayansa da dama.”

“Dole Abubakar Shekau ya fahimci cewa 'ya'ya matan da ya ke amfani da su wajen kunar bakin wake da sunnan addini iyaye da kannenmu ne kuma basu cancanci irin wannan mutuwar ba.”

“Ya kamata ya kuma sani cewa komin dadewa, tilas wata rana zai gurfana a gaban Allah ya yi bayanin zanuban da ya aikata da sunan addinin musulunci, babbu tilasci a addini, Allah ya riga ya dora gaskiya a kan karya.”

“Babu inda Allah ya ambato a cikin ayan Alkur’ani mai girma cewa ya amince dau rai wani dan Adam, bisa wannan ba kada dalilin kashe wanda bai yi imani da addininka ba”, inji AbdulKadir Abubakar.

Idan baku manta ba a baya Legit.ng ta ruwaito cewa Albarnawi ya raba gari da magajin mahaifinsa wato Abubakar Shekau, kimanin shekara daya da suka wuce bayan wani rashin daidaito a tsakanin su. Wannan yasa kowa ya ja nasa rundunar, Shekau ya kama kudancin Maiduguri shi kuma Albarnawi ya koma arewacinta.

Daga cikin kauyukan da Albarnawi yake da iko a halin yanzu sun hada da: Malgwailawanti da Taye da Gwarimiri da Golofori da Gaggau da Charma I da kuma Charma II.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng