Yadda mijina ya rasa ransa a hannun yan ta’adda bayan an sauya masa aiki zuwa Maiduguri – Wata mata ta ba da takaitaccen tarihin mijinta
Duniya budurwar wawa, inda masun iya magana sukayi wa mutuwa lakabi da mai yankar kauna. Hakan ce ta kasance ga wata baiwar Allah da ba’a bayyana sunan ta ba.
Ta bayar da labarin yadda suka fara rayuwar aure da mijinta inda suka kwashe tsawon shekaru ashirin da biyu suna tare da dadi ba dadi.
Mijin nata ya kasance ma’aikacin baki, saboda suna yawan samun canjin wajen aiki daga wannan gari zuwa wani. Cikin wannan hali ne aka tura mijin nata zuwa garin Maidugi babban birnin jihar Borno donn haka suka koma chan da zama.
Bayan komawarsu ne mijin nata ya hadu da ajalinsa sakamakon hari da yan ta’adda suka kai wa ayarin motarsu dake a hanyarsu ta zuwa garin Bama.
Ta fara labarin kamar haka: “Munyi aure tsawon shekaru ashirin da biyu. Na hadu da mijina a garinmu. Mun fito daga kabila guda.
“Mun zauna a garuruwa daban-daban kafin a maida shi Maiduguri. A matsayinsa na ma’aikacin banki yana zuwa ofis ne ba wai a wajen gari ba. Amma wata ranar sai ya bi wani tawaga zuwa Bama a matsayin dan rakiya. Da wuya ya aikata hakan. Bai ma so zuwa ba.
“Yan sa’o’i kadan sai muka samu labarin cewa an kai masu harin bazata. A take hankulanmu gaba daya suka tashi. Saboda bamu san wanene ya rayu ko ya mutu ba. Daga nan sai labaran suka fara rarrabuwa. Dama bamu kan samu labarin abun da ya faru a nan take. Dukkanmu muka dugunzuma wajen neman bayani. Anan ne na gano cewa yam utu a take bayan an harbe shi.
KU KARANTA KUMA: Yawan masara aikin yi a Najeriya sun kuma yawa
“Bazan iya bayyana yadda na ji ba. Ban ma san ta yadda akayi na bar gida ko yadda akayi na kai wajen ba amma na ga kaina ne kawai a tsaye a gaban gawarsa. Haka muka jure radadin sannan akayi masa sutura.
“Bayan jana’izarsa, sai na tsinci kaina cikin wani hali da ban taba mafarki ba. Amma dai na san cewa dole na jure saboda yaran. Ba zai yiwu na fada cikin wani hali ba, yaran zasu wahala.”
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng