Hanyar waraka ta budewa wata mata da ta shafe shekaru 15 tana jinya a jihar Gombe
Bayan tsawon shekaru 15 da wata mata mai sunan Malama Uwani Muhammad, ta shafe tana jinyar rashin lafiya ta yau ne ko gobe, cikon ikon Rabbani hanyar neman kawo karshen wannan tagayyarar tazo mata.
Legit.ng ta ruwaito da sanadin jaridar Rariya cewa, Malama Uwani wadda 'yar asalin jihar Gombe ce an garzaya da ita kasar Morocco domin ceto rayuwarta da ta jima tana wahala.
Rahotanni sun bayyana cewa, Malama Uwani ta shafe tsawon shekaru 15 dinne tana fama da matsalar kashin gadon baya wanda ke dauke da bargo da kuma laka dake kaiwa har cikin kwakwalwa.
KARANTA KUMA: Abdulmumin Jibrin ya kai makura a sakamakon watanni 16 na ci gaba da dakacin da majalisar wakilai tayi masa
A ranar Larabar da ta gabata ne, aka garzaya da wannan mata zuwa kasar ta Morocco, inda take neman daukacin al'umma baki daya da su sanya ta cikin addu'o'in su tare da mika godiyar ga wadanda tuni sun dukufa wajen neman tabbaraki daga Khaliqu.
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng