Hanyoyin kare kai guda 5 yayin doguwar tafiya

Hanyoyin kare kai guda 5 yayin doguwar tafiya

- Karshen shekara alokaci ne na yawan tafiye-tafiye

- Ana yawan samun hatsarin ababen hawa a Najeriya

- Bayan rashin kyan hanya, ganganci da rashin bin dokokin hanya yana kawo karuwar yawaitar hadurra

Jama'a kan yawaita tafiye-tafiye duk lokacin da shekara ta zo karshe. Yayin bulaguro, a jirgi ko mota, akwai dokokin da idan aka kiyaye da su za a samu saukin afkuwar hadurra. Ga biyar daga cikin irin wadannan hanyoyin da zaku iya bi domin kare kan ku.

Hanyoyin kare kai guda 5 yayin doguwar tafiya
Jami'an hukumar kiyaye hadurra ta kasa
Asali: Depositphotos

1. Samun isashshen barci kafin yin bulaguro. Da yawan mutane na wasa da wannan ka'ida mai saukin kiyayewa. Yin doguwar tafiya, musamman ga direba, ba tare da samun isashshen barci ba kan iya zama hadari.

2. Ka san dukkan dokokin hanyar da kake bi. Hakan zai taimaka wajen raguwar samun matsala tsakanin direba da jami'an hukumomin dake aiki a kan titi.

DUBA WANNAN: Sarkin Musulmi ya bayyana 20 ga watan Disamba a matsayin 1 ga watan Rabi'u Asani

3. Ka killace dukkan kayyaki masu muhimmanci ko wadanda kan iya jan hankalin mutane. Zai fi kyau mutum ya bawa kamfanin jigilar kayayyaki kayan sa idan ya kasance suna da yawa.

4. Ka tabbata wani ya san inda zaka. Yana da kyau ka sanar da aboki ko dan uwa inda zaka saboda halin hanya.

5. Ka kasance cikin natsuwa yayin tuki. Sauraron rediyo ko wakoki yayin tafiya yana taimakawa wajen karawa direba natsuwa musamman idan mutum shi kadai yake tafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng