Hotuna: Bikin yaye dakarun sojin kasa karo na 67 daga Zaria
A ranar Talata, 19 ga watan Disamba ne aka gudanar da bikin yaye hafsoshin sojin kasa karo na 67 daga sansanin horas da dakarun sojin kasa da ke barikin Chindit a garin Zaria na Jihar Kaduna.
Sojojin da aka yaye sun gudanar da pareti mai ban sha'awa tare da baje kolin atisaye irin na sojoji daban-daban da suka koya a lokacin da suke samun horaswa. Shugaban gudanarwa Manjo Janar IM Alkali ne ya wakilci Shugaban sojin kasa na Najeriya Laftanat Janar Tukur Buratai a wajen bukin yaye hafsoshin sojin.
Bukin kuma ya samu hallartan wasu manyan baki tare da 'yan uwa da abokan arziki wanda suka zo taya sabbin sojojin murna.
Ga dai hotunan yadda bukin ya kasance a kasa.
KU KARNTA: Mun san bara-gulbi cikin Alkalai, zamu tona musu asiri - Alkalin-Alkalan Bauchi
KU KARANTA: Mun san bara-gulbi cikin Alkalai, zamu tona musu asiri - Alkalin-Alkalan Bauchi
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng