Karanci da wahalar man fetur ta tsallaka wasu sassa na birnin Ibadan
Wasu sassa na birnin Ibadan dake jihar Oyo, sun fara fuskantar kalubale na karancin man fetur da wahalar sa da yake ta ci gaba da ta'azzara a fadin kasar nan.
Legit.ng ta ruwaito da sanadin jaridar Daily Sun cewa, da yawan gidajen mai na birnin Ibadan sun gaza sayar da man fetur din sakamakon karanci da kuma rashin sa da ya fara tunkarar jihar a ranar da ta gabata.
Da yawan gidajen man sun bude domin sayar da sauran ma'adanan man fetur kamar su kalanzir da makamashin gas, sai dai anyi sa'ar gidajen man dake da wadatar sa suka sayar a farashin da bai haura kayyadewar gwamnati ba.
KARANTA KUMA: Dandalin Kannywood: Mansura Isah ta hararowa mata ma'aurata bankayen dake cikin tsafta a gidajen aure
Sai dai al'ummar garin sun zargi wasu gidajen man da 'boyon sa da nufin sai farashin ya harba sama sa'annan su sayarwa da jama'a a tsadance.
Rahotanni sun bayyana cewa, kawowa yanzu farashin na kudin hayar ababen hawa yana a yadda aka saba sakamakon kasuwa ta 'yan bunburutu da bata fara yunkurawa ba.
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng