Yariman Saudiyya mai jiran gado ya sayi gidan da ya fi kowanne tsada a duniya
Rahotanni sun kawo cewa, Yariman kasar Saudiyya mai jiran gado, Salman bin Abdulaziz ya siya gida wanda yafi kowanne tsada a duniya.
An fara gida gidan ne a shekarar 2011 inda aka kammala shi a 2015. Ya mallaki gidan ne a Paris babban birnin kasar Faransa wanda aka saye shi kan kudi dalar Amurka miliyan 301.
Gidan mai suna The Chateau Louis XIV ya shiga hannun Yarima bin Salman bayan ya bayar da kudi har dala miliyan 450 a wajen cinikin da aka yi a watan da ya gabata. A yanzu dai Yarima Muhammad ne ke da mallakin gidan da ya fi kowanne tsada a duniya.
Jaridar New York Times ta bayyana cewa, Asusun Yariman ne ke rike da kulawar gidan wanda na daya daga cikin kadarorinsa manya guda 8.
Mujallar Forbes ta ce, wannan gidan ne gida da ya fi kowanne tsada a duniya a yanzu.
Ga hotunan gidajen a kasa:
KU KARANTA KUMA: Badaru ya ga laifin Lamido kan halin da makarantun Jigawa ke ciki
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng