Cikin Hotuna: Sabuwar fasahar sufuri ta zamani da wani dan Najeriya ya bayar da gudunmuwa
Wani dan kasar Najeriya Oluwatobi Oyinlola, yayi fice a duniya a sakamakon gudunmuwar da kungiyar su ta zakakuran injiniyoyi suka yi na fasahar kera wani jirgi mai sabon salo da fasali kamar na jirgin kasa.
Wannan kungiyar ta injiniyoyi sun shiga gasar daliban jami'o'i na duniya da zasu kawo wata sabuwar dabara ta kera-kere a fasahar sufuri.
Oyinlola da 'yan kungiyar sa sun yi zarra a sakamakon lashe gasar mai take hyperloop Pod competition da aka gudanar a watan Janairu da Agusta na shekarar 2017.
KARANTA KUMA: Dabdalar Karanci da wahalar man fetur: Hukumar NSCDC ta rufe wasu gidajen mai 2 a jihar Neja
Legit.ng ta ruwaito cewa, wannan sabuwar manhajar ta sufuri zata bayar da zabin amfani da ita a madadin sufuri ta jiragen sama, kuma zata kasance hanya mafi sauri idan an kwatanta da jiragen kasa.
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng