Mata masu juna biyu 100 suka rasa rayukan su a jihar Zamfara
- Najeriya ce kan gaba wajen fama da mutuwar mata masu juna biyu inji wani ma'aikacin Asibiti
- Abubakar Danladi ya ce karancin ma’aikata, da rashin ingantattun magunguna ke sa masu juna biyu ke mutuwa a Najeriya
Wani ma’aiakacin asibitin gwamnatin dake Gasau baban birnin jihar Zamfara Abubakar Danladi ya ce a shekarar 2016 jihar Zamfara ta rasa mata masu juna biyu guda 100 ta sanadiyar matsaloli daban-daban.
Danladi ya bayyana haka ne a lokacin wata taro da kungiyar ‘Advocacy Nigeria Network’ ta shirya dan shawo kan matsalolin da masu juna biyu ke fuskan ta a kasar.
Abubakar Danladi yace Najeriya ce kan gaba wajen fama da mutuwar mata masu juna biyu a duniya, musaman yankin Arewa.
Ya ce matsalolin da ke yawan kawo ajalin mata masu juna biyu sun hada da hawan jinni, yawan sinadarin cin ‘Protein’ da akan samu a fitsarin mace mai ciki wato ‘Eclampsia’ wato zuban jini.
KU KARANTA : Injiniyoyi 2 yan Najeriya sun kera nau’arar janareta da baya amfani da man fetur ko gas
Danladi yace bai kamata irin wadannan matsaloli su rika fin karfin likitoci Najeriya ba, amma saboda karancin ma’aikata, da rashin ingantattun magunguna yasa masu juna biyu ke mutuwa a kasar.
Daga karshe Danladi yayi kira da kungiyoyi masu zaman kansu da kafafen watsa labaru na Najeriya da su yawaita tunatar da gwamnati muhimmancin kula da lafiya mutanen kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng