Shugabannin kungiyar Izala sun dawo Najeriya (hotuna)
- Shugabannin kungiyar Izala sun dawo Najeriya daga kasar Burtaniya
- Jirgin da ya dauko su ya saka ne a babban birnin tarayya Abuja
- An hango babban sakataren kungiyar Sheikh Kabir Haruna Gombe tare da shugaban Kungiyar Sheikh Abdullahi Bala Lau cikin fara’a
A safiyar yau Talata, 12 ga watan Disamba jirgin day a dauko manyan malaman kungiyar Izala daga kasar Burtaniya ya sauka a babban filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe.
Jirgin wanda yake dauke da Shugaban Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau, tare da Sakataren kungiyar Sheikh Kabiru Gombe, ya sauka a babban birnin tarayya Abuja.
KU KARANTA KUMA: Baza’a iya tsige shugaban kasar Najeriya ba a karkashin kundin tsarin mulkin 1999 - Dogara
An hango babban sakataren kungiyar Sheikh Kabir Haruna Gombe tare da shugaban Kungiyar Sheikh Abdullahi Bala Lau sun sauko cikin fara'a suna ta fadin "Alhamdulillah" wanda Alamu ke nuna sun samu gagarumar nasara a bulaguron da sukayi na aikin Da'awa a kasashen Turai.
Ga hotunan a kasa:
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng