Yabon gwani ya zama dole: Matasan Arewa sun karrama Gani Adams
- Wata kungiyar matasa mai fafutukar tabbatar da zaman lafiya ne ta karrama shi
- Ta karrama shi ne da taken Yariman Matasan Arewacin Najeriya da kuma mika masa lambar yabo
- Kungiyar ta ce Adams madubin dubawa ne game da kyawawan dabi'u
A ranar Juma'a ne Babafemi Ojudu, mai ba wa Shugaban Kasa Buhari shawara ta musamman game da harkokin siyasa, ya bayyana Gani Adams na al'ummar Yarbawa, a matsayin mai fafutukar neman 'yanci. Ojudu ya kuma ce Adams ya cancanci sarautar sa na Aare Ona-Kokanfo.
Ojudu ya ziyarci Adams ne a gidan sa na Abuja yayin da Kungiyar Matasan Arewa masu Neman Wanzuwar Zaman Lafiya da Shugabaci na Gari, su ka karrama Adams da taken Yariman Matasan Arewacin Najeriya da kuma mika masa lambar yabo.
A nan ne Ojudu ya taya Adams murna, ya kuma bayyana cewan gaskiyar sa da kuma rikon amanar sa ne su ka kawo masa wadannan kyawawan sakamakon.
KU KARANTA: Labari da duminsa: Jimi Agbaje ya janye daga takarar shugabancin PDP
Shugaban kungiyar, Umar Faruk Lawal, yayin gabatar da lambar yabon ga Adams, ya ce lambar yabon ya na nuni ne ga dattako da ayyukan cigaban al'umma da Adams ya gudanar. Ya kuma ce Adams madubin dubawa ne game da kyawawan dabi'u.
Shi kuwa Adams, kira ya yi ga matasan da su guji tsauraran ra'ayoyi don kawar da yaduwar muggan kungiyoyi kamar irin Boko Haram. Ya kuma ce wannan ziyara da su ka kai ma sa zai tabbatar wa 'yan Kudu mazauna Arewa cewan su na zaune cikin aminci.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng