Allah ya tabbatar: Manoman Najeriya zasu karya farashin Masara da kashi 50

Allah ya tabbatar: Manoman Najeriya zasu karya farashin Masara da kashi 50

A yunkurin ta na hana cigaba da shigo da masara daga kasashen waje, kungiyar manoman masara na Najeriya, a karkashin shugaban ta, Kwamared Retson Tedheke sun samar da matakan rage farashin masara da kashi 50.

Retson yace hakan zai yiwu ne kadai, idan gwamnati ta cigaba da samar da kayan aiki a gonakai, don tallafa ma manoman, inda yace a yanzu akwai sama da hekta 2000 da ake girbe masara a yanzu haka, kamar yadda ya shaida ma Leadership.

KU KARANTA: Abin kunya: Jami’in hukumar kare hadɗura ya gwada ƙwanji da wata mata a kan titi

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Retson yana fadin zuwa damina mai zuwa, ana sa ran manoman masara a Najeriya zasu noma sama da hekta 5000.

Allah ya tabbatar: Manoman Najeriya zasu karya farashin Masara da kashi 50
Masara

A yanzu haka farashin tan na Masara na tsakanin 80,000, 95,000 da 120,000, a haka ma Retson yace sumin tabi ne, matukar gwmanatin shugaba Buhari zata cigaba da kokarin da ta faro game da aikin noma.

Daga karshe Retson ya yaba ma shugaba Buhari, tare da shawartarsa akan hanyoyi da ya kamata gwamnati ta bi wajen inganta aikin noma, ta yadda farashin kayan abinci zai fadi warwas.

“Idan Buhari na son ceto kasar nan daga yunwa, toh ya samar da tarakta dayawa ga manoman Najeriya, wannan kadai zai rage farashin kaya gona da kashi 30. Kuma zai rage ma manoma wahalwalu samu rance.” Inji Retson.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng