Zargin karkatar da naira biliyan 1: Kotu ta wanke Yariman Bakura da soso da sabulu

Zargin karkatar da naira biliyan 1: Kotu ta wanke Yariman Bakura da soso da sabulu

- Kotu ta fatattaki karar ICPC da ta shigar da Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura

- ICPC na tuhumar tsohon gwamnan ne da laifin satar kudi naira biliyan guda

Wata babbar Kotun jihar Zamfara dake garin Gusau ta sallami wata kara kan zargin cin hanci da rashawa da hukumar yaki da rashawa da dangoginta, ICPC, ta shigar a kan tsohon gwamnan jihar Zamfara.

Tun a watan Janairun shekarar 2016 ne ICPC ta maka Sanata Yarima gaban kotu, inda take zarginsa da kakartar da naira biliyan daya, wanda aka ware da nufin gyaran madatsan na Gusau, inda tace kudin an samo su ne daga bashin Banki.

KU KARANTA: Majalisar tarayya ta sahhale ma gwamnatin jihar Kaduna ciyo bashin dala miliyan 350

Daily Trust ta ruwaito mai shari’a Bello Muhammad Tukur yayi watsi da dukkanin tuhume tuhume 19 da ICPC ke tuhumar Sanata Yarima akan su, bayan sauraron karar lauyan wanda ake kara, inda yace Yarima bai tama yi ma kan sa, Abokai ko yan uwansa alfarma ba a zamanin mulkinsa.

Zargin karkatar da naira biliyan 1: Kotu ta wanke Yariman Bakura da soso da sabulu
Ahmed

Dayake zantawa da majiyar Legit.ng, Sanata Ahmad Sani ya yaba da hukuncin Kotun, inda yace gaskiya ta yi halinta, dama can shi ya san bai tafka wani ta’asa ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng