Manyan ‘Yan wasan Duniya na gudun haduwa da Najeriya a World Cup
– Neymar na Brazil ya godewa Allah da bai hadu da Najeriya ba
– Wasu dai na gudun ‘Yan Super Eagles a Gasar cin kofin Duniya
– Kocin Kasar Kuroshia ma dai bai ji dadin hada su da Najeriya ba
Labari ya zo mana cewa har Kasar Brazil tana tsoron haduwa da Najeriya a Gasar World Cup da za a buga a shekara mai zuwa 2018 na cin kofin Duniya a kasar Rasha. Zlatko Dalic watau Kocin Kasar Kuroshia ma yace yana jin tsoron Najeriya.
Babban Dan wasan Brazil Neymar Jr. ya bayyana cewa ya ji dadi da Kasar sa ba ta hadu da Najeriya a wasannin rukuni ba a Gasar. Ana dai ji da babban ‘Dan wasan gaban na Kungiyar PSG watau Neymar a Duniyar kwallon kafa.
KU KARANTA: Sergio Ramos ne ya fi kowa shan jan kati a La-liga
RFI Hausa ta rahoto wannan labara inda Neymar ya nuna farin cikin sa bayan da yaga cewa Najeriya da Brazil ba su fado cikin sahu guda ba a jadawalin Gasar da aka fitar kwanan nan. Najeriya za ta kara karawa ne da su Argentina.
Neymar yace sun samu sauki wajen rashin haduwa da Najeriya da kasashen Afrika inda yace kasashen na Afrika na amfani da karfin tuwo yayin da aka shiga filin wasa ana gwabzawa. Neymar zai kara da irin su Kasar Costa Rica da Sabiya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng